Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar litini

Published

on

Jama’a barka ku da war haka, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na Jaridu ranar litini.

  1. A daren Lahadi ne aka shiga firgici yayin da wani gini ya rufta a kan titin Adeleye, Lady Lark, yankin Bariga a jihar Legas. Yara biyu sun mutu, yayin da manya uku suka samu raunuka daban-daban. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da faruwar lamarin.
  2. Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, ya ce fitaccen dan fashin daji nan, Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar a wani bangare na kokarin kawo karshen ‘yan fashi da makami a jihar Arewa maso Yamma.
  3. Alamu sun bayyana a jiya cewa gwamnatin tarayya na iya duba yiwuwar haramta kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, idan har ta kasa janye yajin aikin da aka tsawaita bayan tayi mata tayin. Gwamnatin tarayya ta kuma amince da karin Naira biliyan 100 ga bangaren jami’o’in a wani bangare na fahimtar juna a sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.
  4. Manoman karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun amince su biya makudan kudaden da ‘yan fashin daji suka kakaba masu domin su shiga gonakinsu. A cewar shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Usman Kasai, yan bindiga sun dorawa manoman haraji na miliyoyin naira.
  5. Wasu ‘yan bindiga da ke yin barna a sassan Kudu-maso-Gabas sun yi garkuwa da wasu ‘yan uwa mata na cocin Katolika a jihar Imo. An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a babbar titin Okigwe-Enugu yayin da wadanda abin ya shafa ke kan hanyarsu ta zuwa taro a safiyar Lahadi.

Zafafa Labarai