Countdown
Connect with us

Illimi

Malaman KASU Sun Yi Watsi Da Umarni Komawa Makaranta, Sunce Har Sai An Janye Yajin Aiki

Published

on

Jami’ar Jihar kaduna

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, reshen jihar Kaduna, KASU, ta bayyana a ranar Lahadi cewa ba ta janye yajin aikin da take yi ba kamar yadda mahukuntan jami’ar suka yi ikirari.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar Peter Adamu da mataimakin sakatare Akos Ibrahim suka sanyawa hannu tare da bayyanawa manema labarai a Kaduna.

Kungiyar ta nesanta kanta da sanarwar da mahukuntan jami’ar suka fitar na neman dalibai da malaman jami’o’in da su koma harkokin ilimi a ranar 9 ga watan Mayu.

A cewar malaman, umarnin ya saba wa matsayin kungiyar a gwagwarmayar da take yi a halin yanzu.

“Bayanin umarnin hukumar jami’ar kaduna wanda ta fitar na baya baya nan da yake ta yaduwa a shafukan sada zumunta me cewa jami’ar KASU ta fice daga yajin aikin da ke gudana ne ya ja hankalin kungiyar malaman jami’oi rashen jami’ar kaduna (ASUU-KASU).

“Musamman, sanarwa da akayi a ranar 26 ga watan Afrilu , 2022, wanda ya umurci dukkan membobin ma’aikata da daliban jami’ar da su koma harkokin ilimi a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, 2022.

“Ya zama wajibi a wannan lokaci a fayyace hakan da kuma sanar da daukacin jama’a tare da illimantar dasu cewa kungiyar malaman jami’oi rashen KASU (ASUU-KASU) ta nesan ta kanta daga sanarwar da aka ce shugabannin jami’ar sun fitar.

“Wannan kawai ya saba wa matsayin kungiyar a cikin gwagwarmayar da ta ke yi a halin yanzu,” in ji malaman.

A cewarta, hukumar gudanarwar jami’ar na da ‘yancin bude jami’ar yayin da ‘ya’yan kungiyar kuma suke da hakki na ci gaba da yajin aikin da suke yi.

“Yana da kyau a lura cewa hukumar gudanarwar jami’ar ba ta da ikon magana da yawun bakin kungiyar ko fitar da sanarwa a madadin kungiyar.

“Don haka kungiyar ta shawarci iyaye dalibai cewa kada su bari ‘ya’yansu su dawo makarata har sai an dakatar da yajin aikin dake gudana.”

Kungiyar ta bayyana cewa yajin aikin da ake ci gaba da yi shi ne maslaha ga tsarin jami’o’in kuma babu wata barazana da za ta sa reshen su janye wa daga fafatawa a halin yanzu.

Ya bayar da hujjar cewa shigar ma’aikata a kowace gwagwarmayar masana’antu doka ce kuma ta tsarin mulki kamar yadda aka tsara a sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara.

Ya kara da cewa Kungiyar Kwadago ta Duniya da ma’kala ta 20 na Yarjejeniyar Hakkokin Dan Adam ta Duniya, na shekarar 1948, sun kuma amince da ‘yancin yin tarayya da ma’aikata.

Kungiyar ta ce duka dokokin biyu sun tabbatar da cewa ma’aikata su kasance masu ‘yancin shiga kowace kungiya ba tare da tilastawa ma’aikatansu ko wata hukuma ta tilasta musu ba.

“Saboda haka shigar malaman jami’ar KASU yajin aikin ASUU ya dace kuma ya yi daidai da dokokin kwadago na kasa da kasa.

“Muna so mu gode wa mambobinmu saboda jajircewa a wajen gwagwarmaya.

Zafafa Labarai