Countdown
Connect with us

Labarai

YAJIN AIKI: Majalisar jihar Kaduna zatayi matukar kokarin domin kawo karshen yajin aikin ASUU – Isaac Auta

Published

on

mataimaki Kakakin majalisar Jihar Kaduna, yayin ganawa da manema labarai. Hoto: Channels Tv Asali: Channels Tv.

Mataimaki kakakin majalisa jihar Kaduna, Isaac Auta, ya ce majalisar Jihar Kaduna zatayi bakin kokarin ta domin ganin ankawo karshen yajin aikin kungiyar malaman jami’oi wato ASUU.

Auta ya bayana hakan ne a lokacin da ya tarbi tawagar masu zanga-zanga kawo karshen yajin aikin a Kaduna, wanda kungiyar NLC ta shirya, da yafara gudana yau talata.

A yayin jawabin sa, mataimaki kakakin majalisa jihar Kaduna, yace, Ina tabarta muku majalisa jihar Kaduna zata duba lamarin bukatunku yadda ya kamata.

” A madadin Kakakin majalisa jihar Kaduna dakuma sauran mambobin majalisar, ina mika godiyata da hakuri da kuka nuna, kuma majalisar jihar Kaduna na bayan ku, burin mu shine muga daliban mu sun koma bakin karantun su.” Inji shi.

” Ina tabatar muku zamuyi iyayin mu nagani an biya muku bukatunku, sabida kishi da son kasa da kakakin majalisa ke dashi, kuma amatsayin sa na Shugaban ‘yan Majalisu jihohin arewa, yanzu haka yana Abuja domin ganin a shawo Kan lamarin.”

Auta, yanuna takaici kan yajin aikin dake gudana inda yabar dalibai zaune a gida na tsawon watanin biyar, ya kumayi kira ga gwamnati taraya da ta amince da bukatun malaman.

Kungiyar malaman jami’oi ASUU ta shafe kimani watanin biyar suna gudanar da yajin aiki a fadin Nijeriya.

Wanda hakan yasa kungiyar kwadago ta kasa NLC ta shirya zanga-zanga lumana na kwana biyu domin kira da a kawo karshen yajin aikin da aka shafe watanin anayin sa.

Zafafa Labarai