Countdown
Connect with us

Labarai

Ma’aikata a Kaduna sun gudanar da addu’o’i na musamman don neman taimakon Allah Ya inganta yanayin aiki a jihar

Published

on

A jiya ne ma’aikatan jihar Kaduna suka gudanar da addu’o’i na musamman a masallacin Juma’a na Sardauna Memorial College da ke cikin garin Kaduna, inda suka nemi taimakon Allah ga ma’aikatan jihar.

A jawabinsa na Juma’a na mako mako, Babban Limamin masalacin Malam Liman Sani, ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa ma’aikata addu’a, inda ya roki Allah da ya taba zukatan shuwagabanni gun jinkai ga ma’aikata, tare da kyautata musu rayuwarsu.

Limamin ya kuma yi addu’ar zaman lafiya da hadin kai da ci gaban Jiha da kasa baki daya.

Shugaban tawagar, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Kaduna, Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya ce an gudanar da irin wannan addu’a a ranar Lahadin da ta gabata a wata coci da ke jihar.

Ya ce an yi addu’ar Allah ya baiwa ma’aikata damar gudanar da bukukuwan ranar Mayu ba tare da tangarda ba, tare da samun nasara a fafutuka daban-daban da shugabannin majalisar ke yi a madadin ma’aikata.

Suleiman ya yi kira ga ma’aikata da su sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban jihar.

Wani bangare na ayyukan da aka jera domin bikin ranar Mayu shi ne taron karawa juna sani, addu’o’i a coci-coci da masallatai, inda za a gudanar da bikin na karshe a ranar 1 ga Mayu, a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.

Zafafa Labarai