Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Lekcara ta kubuta, direba da yarta na rike a hanun ‘yan bindiga

Published

on

A ranar talata ne ‘yan bindiga da suka sace lekcara makarantar kimiya da fasaha ta gwamnati taraya dake Kaduna (Kaduna Polytechnic), Dr. Ramatu Arbashi, su ka sake ta.

Saidai, yarta Ameera, da direban ta nacan a tsare a hanun ‘yan bindiga.

In za a tuna, a ranar 24 ga watan Afrilu, 2022 ne wasu ‘yan bindiga sukayi garkuwa da lekcara, yarta da kuma direban ta, akan hayar mariri dake karamar hukumar Lere.

Bayan dawo wa daga raba talafi ga marasa karfi a karkashin gidauniyarta me suna “Barkindo Rahama Initiative”, inda daga baya ‘yan bindiga suka nema naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Wani ma’aikaci gidauniyar, Abdullah Ismail Abdullah, ya tabatar da kubutar Dr. Arbashi, a ranar talata, sai dai bai fada nawa a ka biya a matsayin kudin fansa ba.

Yace ” bayan sun sake ta a daren ranar talata, mun garzaya da ita asibiti domin duba lafiyar ta.

Saidai haryan zu yarta da direban ta nacan tsare a hanu ‘yan bindiga.

Zafafa Labarai