Countdown
Connect with us

Siyasa

Lawal Adamu Mr. La, ya lashe zaben fidda gwani takara kujerar senata kaduna ta tsakiya a jam’iyar PDP

Published

on

Lawal Usman Adamu Mr La Hoto: Mr La Asali: Facebook

Rahotonin sun bayana cewa Lawal Adamu Usman, wanda ake wa lakabi da Mr. La, shi ne ya lashe zaben fidda gwani kujerar takara senata kaduna ta tsakiya, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Andai gudanar da zaben ne a ranar laraba, 23 ga watan Mayu, 2022, akala Yan takara bakwai ne suka fafata a zaben daya hada da maza 6 mace daya.

Mr. La, ya lashe zaben ne da samu kuri’u 99, yayin da Ibrahim Usman Sardauna , ya samu kuri’u 84, sen. Musa Bello, ya samu 43, (Dr) Ahmad Inuwa, 15, Usman Muhammad, 2, Hajiya Talatu kuri’u 5. Kamar yadda sakamokon zaben ya bayana.

Mr. Lah, shi ya lashe zaben fidda gwani a zaben 2019, saidai ya sha kayi a baban zabe inda Sanata Uba Sani na Jami’ar APC, ya lashe zaben.

Mr. Lah, ya kasance dan siyasa na farko daya biya wa dalibai kudin makarata a karkashin gidauniyar sa Mai suna Lawal Usman Adamu Foundation, tun bayan karin kudin makarata da gwamnati Jihar Kaduna tayi a shekarar data gabata.

Dalibai da dama ne suka samu talafin kudin makarata, a tsakanin makarantu gaba da sekondiri malakin Gwamnatin Jihar Kaduna, Kama daga Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Makarantar Kimiya da Fasaha ta Nuhu Bamali Politeknic, Zaria, Kwalejin Illimi dake Gidan Waya da sauransu.

Zafafa Labarai