Countdown
Connect with us

Labarai

Kyandar Biri: An Umarci Mahajata Jihar Kaduna da su guji ziyara da ba gaira ba dalili

Published

on

A jan kune mahajatan 2022 na jihar Kaduna da su guji ziyara Mara dalili, ziyara marasa lafiya dake jinyar ciwon fata da wahalar nufamshi, domin guje wa kamuwa da cutur kyandar Biri.

Ciyama Din Kula Da Lafiya Alhazai Na Jihar Kaduna, Dr. Abdulrasheed Ibrahim, ne yayi kiran yayin taron ganawa da masu harkan kiwon lafiya daga Ministri Lafiya Jihar Kaduna.

Dukda Jihar Kaduna bata da masu dauke da cutar, wakilan kasar Saudiya ne suka umurci da ayi gwajin cutar ga duk wani Dan Nijeriya.

” Muna son dukan Mahajata mu su kasan ce a gun dasuke, su daina ziyara Mara dalili, ko ziyarta masu ciwon fata, tari, wahalar numfashi domin sune alamun cutar kyandar biri. Yin cudanya tsakanin Mai dauke da ciwo na iya sa a kamuwa da cutar.” Inji shi.

A cewar sa, Duk Mahajaci da aka samu da alamar cuta za a tura shi domin duba lafiya sa, in har bincike ya tabatar ya na dauke da cutar, to za akilace shi.

” Sanan duk Mahajaci da ke dauke da cutur ba zai samu damar zuwa aikin haji ba ko Kuma za a kilace shi, sai inhar ya tsalake matakin ciwon bayan kilacewa, sanan daga baya zai tafi.”

Zafafa Labarai