Countdown
Connect with us

Siyasa

Kwamishinoni Mata sunfi maza yawa a kaduna cewar Mataimakiyar Gwamna

Published

on

Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe Hoto: Governor of Kaduna State Asali: Facebook

Mataimakiyar Gwamna Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayana cewa a yanzu haka kwamishinoni Mata sunfi maza yawa a jihar.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa akala kwamishinoni 17 ne dake taya Gwamnati aiki a Jihar, wanda 9 daga ciki su Mata ne takwas Kuma maza.

Balarabe ta yabawa gwamna Nasir El-Rufai kan wannan rawar da ya taka, a lokacin da take rantsar da wasu sabin masu mukamai na siyasa a ranar Laraba, Balarabe ta ce “a halin yanzu jihar Kaduna ce guri domin mata a Najeriya.”

Ta ce yawan kwamishinonin mata a Kaduna “babu shakka shine mafi kyau a Najeriya da kowace kasa a Afirka”.

Ta kuma shawarci duk matan da aka nada da su Sanya gwamna alfahari da haka tare da bude kofa ga mata masu yawa su shigo.

Zafafa Labarai