Countdown
Connect with us

Tsaro

Kuyi Hakuri Ku Ji Tsoran Allah Ku Sake Mutane Da ku Kama A Jirgin Kasa Zuwa Kaduna – Dr. Ahmad Gumi

Published

on

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da wasu fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, da su kubutar da su “don girman Allah”.

Hakan na zuwa ne bayan da malamin ya kafa wata kungiya mai fafutuka da nufin kwato tare da kare hakkin Fulani makiyaya.

Gumi ya sanar da kafa kungiyar mai suna ‘Nomadic Rights Concern’ a lokacin wa’azin watan Ramadan a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. A cewarsa, hakan zai jawo hankali ga cin zarafi da take hakkin Fulani makiyaya.

“Muna kira gare ku (’yan bindiga) da ku ji tsoron Allah, ku dauki tafarkin zaman lafiya. Ya kamata ku yi koyi da ɗayanku da ya saki dukan waɗanda ya kama a ƙarƙashinsa ba tare da wani sharadi ba; ya tuba ya kuma nemi gafarar Allah,”

Inza a tuna dai a ranar 28 ga watan maris, din shekarar 2022 ne Wasu ‘yan ta’adda suka dasa bom a kan titin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna tare da bude wata ma jirgin dake kan hanyar sa ta zuwa Kaduna wanda yayi sanadiyar mutuwa tare da raunata wasu fasinjoji, inda kuma ‘yan ta’adda sukayi garkuwa da wasu ciki harda Yara, tsofafi da Kuma mata da maza.

Rohotonin baya baya nan sun Tabatar dacewa daya ga cikin Mata masu ciki da ‘yan ta’adda sukayi garkuwa dasu ta haihu a hanusu.

Zafafa Labarai