Countdown
Connect with us

Tsaro

Kungiyoyin Boko Haram da Ansaru na neman mabiya ta hanyar raba kyaututuka a Kaduna – Kwamishina Tsaro

Published

on

Kwamishina Tsaro Na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, Hoto: KDSG Asali: Facebook

Gwamna Jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufai, ya nuna damuwar sa matuka Kan ayukan kungiyoyin ta’adacin a Jihar.

Elrufai, ya bayana hakan a yayi taron bada rohoton sha’ani tsaro, na quarter farko na shekara 2022 ga Kaduna Security Council.

Gwmana, ya bayana cewa ‘yan ta’adan na tasowa ne daga yankin arewa maso gabas zuwa arewa ta yanma don tarwatsa yankin.

Kwamishina Tsaro Da Harkoki Cikin Gida, Samuel Aruwan, shima ya bayana cewa, yan zu haka ‘yan kungiyar Ansaru da Boko Haram sun shiga wasu yan Kuna karamar hukumar Binin Gwari, da kuma Giwa.

Aruwan, ya Kara dacewa kungiyar na neman mabiya ne ta hanyar rabawa mazauna kyaututuka.

A halin yanzu, a qalla mutum 360 ne ‘yan ta’ada suka kashe a sassa daban daban na jihar Kaduna, daga watan Janairu zuwa Afrilu 2022. Inji Aruwan.

A qalla mutum 214 ne suka rasa rayukan su a yankin kaduna central senatorial zone, hakan ya sa sukafi kowane zone fuskanta matsalar ‘yan ta’adda. Cewar Kwamishina.

Aruwan, ya qara da cewa akala mutum 1389 ne a kayi garkuwa dasu a cikin quarter farko, wanda ake kan dubawa, ciki hada mutum 62 da aka sace a harin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna.

Zafafa Labarai