Countdown
Connect with us

Wasanni

Kungiyar wasa ta Chelsea ta salame Tuchel

Published

on

Kungiyar wasan kwalon kafa ta Chelsea ta salami Thomas Tuchel, a ranar laraba, biyo bayan rashin nasara datayi a gasar “Champion League” a ranar talata a hanu kungiyar Dinamo Zagre, inda aka tashi 1:0.

Kungiyar ta sanar da korar a wani walafi da tafitar a shafinta na yanargizo.

Sanarwa tabayana cewa,” Kungiyar kwalon kafa ta Chelsea a yau ta yi ban kwana da baban kocin ta Thomas Tuchel.

” Ma’aikata masu bada horo na tawagar kungiyar ne zasu cigaba da jan akalar kungiyar, kama daga bada horo da shirya wasani dake tafe kafin nadin sabon baban mai bada horo.

” Babu wani Karin bayani har sai an nada baban Mai bada horo da zai jagoranci tawagar kungiyar.

Zafafa Labarai