Countdown
Connect with us

National

Kungiyar mallaman jami’oi ASUU ta tabatar da tsawaita yajin aikin da takeyi

Published

on

Kungiyar mallaman jami’oi na Nijeriya, ASUU ta amince da cigaba da yajin aiki da takeyi har sai baba ta gani.

Wanan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar Prof. Emmanuel Osodeke, ya fitar a ranar litini.

A ranar dai lahadi me kungiyar da yi taro da shugabannin zartawa na kungiyar Kan makomar yajin aikin a Abuja.

Sanarwa ta zargi gwamnati da nuna halin ko in kula kan gani an shawo kan matsalar da take faruwa tsakanin gwmanati da kungiyar mallaman jami’oi.

ASUU ta far gudanar da yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Faburairu, 2022 a matsayin yajin aikin gargadi, inda ta kara tsawaita yajin aiki domin ba gwamnati dama da su yi abin da yadace .

Kungiyar ta kara ba da karin sati hudu, domin ko za asamu matsalaha, ama abin yaki cin tura.

Yajin aikin sai baba tagani da kungiyar ta tafi zai fara aiki ne a da misalin karfe 12:00 na daren litini.

Zafafa Labarai