Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Kungiyar Jaja Solidarity Forum Ta Ba Da Gudumawar Motocin Domin yi Ma Senata Uba Sani Kampe

Published

on

Uba Sani, a gaban Motocin Hoto: Kaduna Response Team Asali: Facebook

Kungiyar Jaja Solidarity Forum, ta bayar da gudunmawar matoci don yin ma Sanata Uba Sani Kampe, kungiyar wanda shugaban karamar hukumar kudan, Hon. Shuaibu Bawa Jaja, ke jagoranta.

Motocin sun hada da motoci kirar Volkswagen (golf), pegeote 206, rufe da pastocin Dan takarar Senata Sani, Abdu kwari tareda Shuibu Jaja.

Uba Sani, shine dan takara da Gwamna Elrufai, ya tsaida a matsayin wanda zai gobza takara kujerar gwamna Jihar kaduna a zabe 2023 a jam’iyar APC.

Duk da zabin Gwamna ya haifar da cece kuce tsakanin Yan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyar APC, inda wasu suke ganin hakan ya ci karo da tsarin dimokradiyya, a don haka a bari kawai a gobza zaben fidda gwani.

Zafafa Labarai