Countdown
Connect with us

Tsaro

Ku Biya Kudin Fansa A Sako Mutane Da Akayi Garkuwa Dasu A Jirgin Kasa Zuwa Kaduna, Gumi Ga Gwamnatin Taraya

Published

on

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

Baban malamin adinin musulunci, a kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya shawarci gwamnatin taraya da ta biya kudin fansa a sako mutane da akayi garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja zuwa kaduna.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa Gumi, yayi Kiran ne a lokacin da ya halarta taron adua na musaman da kungiyar Jam’iyyar Matan Arewa (JMA), ta shirya a ranar Alhamis a kaduna.

Gumi, ya Kara dacewa ” dubi yarda mutane ke biyan makudan kudade gun siyan fom din takara, maimakon subiya kudin fansa ga talakawa Nijeriya, Wanda basu dashi a sake su daga hanu masu garkuwa da mutane, ko mai suke bukata ku basu domin su sake mutane da suka tsare dasu.”

” Kuna da damar daukan matakai da suka dace da su a lokacin da suke tsare da mutane, saidai akwai bukatar ku bi a hankali tayada Wanda ake tsare dasun ba su cutu ba. A cewar sa.”

In za a tuna dai a ranar 28 ga watan maris, ne Yan ta’adda suka Kai Hari Kan jirgin kasa wanda ke Kan hanyar sa ta zuwa kaduna, inda Suka Kashe mutum 9 ta re da raunata wasu da sace wasu fasinjoji.

Anasa jawabin, Shugaban Mabiya adinin Kirista, rashen Jihar Kaduna, Rev. Joseph Hayab, ya kalubanci shuwagabanin da su tabatar sun kubutar da wanda akayi garkuwa da su tare ganin sun dawo cikin iyalensu lafiya.

Shugaban kungiyar, Hajiya Rabi Saulawa, tace sun shirya taron adu’a ne don rokan Allah ya kubutar da Wanda akayi garkuwa dasu tare da yima kasa adu’a baki daya don samun zaman lafiya.

Zafafa Labarai