Countdown
Connect with us

Illimi

KSSLB ta bayana yadda ta zakulo dalibai 1,251 da aka biya wa kudin makaranta

Published

on

Hukumar bada talafi da bashi kudin karatu na jihar Kaduna ta bayana yadda ta zakulo dalibai 1,251 da aka biya wa kudaden makaranta a makarantu gabada sekondiri uku malakin gwamnatin jihar.

Shugaban hukumar Hassan Rilwanu, ne ya bayana hakan a yayin fira da gidan radio na Vision FM dake Kaduna a ranar asabar.

Rilwanu yace rukuni talafi kala biyu ne wanda daliban suka ci moriyar sa, wanda yahada da rukuni talafi dalibai masu hazaka da kuma rukuni talafi karatu dalibai marasa karfi.

Yace sun tura makarantu ne domin bada sunayen dalibai da suke da CGPA 4 zuwa sama a tsarin CGPA 5 da kuma 3.50 zuwa sama a tsarin CGPA 4.

Sai kuma a bangaren marasa karfi sunyi anfani da soshiyal rigista jihar Kaduna ne na jerin sunayen dalibai mabukata.

Inda suka tura sunayen ga makarantu su domin a fada wa daliban su cike bayana su a shafin yanargizo bada talafi na hukumar.

Rilwanu ya karada cewa, kawo yanzu sunfara da makarantun gaba da sakondari uku ne wanda suka hada da Jami’ar Kaduna (KASU), Nuhu Bamali polytechnic, Kwalejin Illimi Gidan Waya.

Yace kuma zasu cigaba da tantancewa tare da bada talafi karatu ga duk wani dalibi da ya chanchanta a makarantu gaba da sekondiri dake ciki da wajen jihar Kaduna.

Zafafa Labarai