Countdown
Connect with us

Ko Kun San ?

KDSG za ta kashe sama da #3bn gun daukar nauyin karatu dalibai a shekara 2022

Published

on

Gwamnati Jihar Kaduna a shekara 2022 zata kashe #3,228,536,000 gun daukar nauyin karatun dalibai wanda suka chanchanta a fadin jihar kama da karatu a gida da kasashen waje.

Bayanin kashe kudin na kunshe ne a cikin kudin kasafin jihar Kaduna na shekara 2022.

Inda ake sa rai gwamti zata kashe #2,102,005,000 kan talafi karatu na kasashen waje, yayin da zata kashe #1,126,531,000 a harkokin talafi karatun cikin gida. Wanda jimilan kudi yakama #3,228,536,000.

Kasafin dai na karkashin kasafin hukumar kula da bada bashi, talafi na Jihar Kaduna na shekarar 2022.

Hukumar bada rance da talafi karatu na Kaduna Scholarship And Loans Board, ke da alhakin tantance daliban domin gani sun chanchanta cin gajiyar talafin.

Don haka dalibai jihar Kaduna kada ayi kasa agwiwa a ziyarci shafin bada talafi da rance na jihar Kaduna, domin karin bayini yadda za adace da cin gajiyar talafin.

Zafafa Labarai