Countdown
Connect with us

Labarai

KDSG ta rattaba hannu kan yarjejeniya tare da Kamfanin Doctors Clinic UAE don Samar da asibiti mai gado 300

Published

on

Gwamnati jihar Kaduna karkashin jagoranci Elrufai, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tare da Kamfanin Doctors Clinic na Hadaddiyar Daular Larabawa.

A matsayin wani bangare na matakan da za a dauka don samar da asibiti mai gadaje 300.

Abokan haɗin gwiwar za su gudanar da asibitin domin samar da ingantaccen aiki kuma mai dorewa.

Wanda asibiti zai yi gogaya da sauran asibitoci ingantatu na ƙasashen duniya.

Asibitin zai kasance yana da sassa 26, gun tiyata 6, ICU, da kayan aiki cututtukan zuciya da magungunan da sauran su.

Har ila yau gwamnati Kaduna, ta kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Elekta, don siyan kayan aikin da za a yi amfani da su don maganin nukiliya da cibiyar cutar sankara a asibitin.

Wanda ana sarai hakan zai fadada karfin a kasar don gani an magance cutar daji.

Zafafa Labarai