Countdown
Connect with us

Labarai

KASU ta maida martani kan furucin shugaban kungiyar ASUU

Published

on

Hukumar jami’ar Kaduna ta maida martani ga shugaban kungiyar ASUU na kasa, Prof. Emanuel Osodeke, kan kiran jami’oi jihohi marasa inganci da chanchanta.

Bayanin hakan na kunshe ne a wani sanarwa da jami’i mai hulda da Jama’a na jami’ar, Adamu Bargo ya fitar a ranar asabar Kaduna.

A cewar sanarwar, ta bayyana a fili cewa, da irin wannan furuci, ASUU ba ta fafutukar ganin an inganta tsarin ilimi a Najeriya, sai dai kawai don raɗin kansu tare da abinda zasu samu.

Sanarwar ta yi mamakin ko Farfesan Kimiyyar Ƙasa ya fahimci ainihin abin da kalmar “quack” ke nufi.

Kalmar Quack yana nufin mutumin da rashin gaskiya ya yi ikirarin cewa yana da ilimi da fasaha a wani fanni wanda ba shi da tushe, kamar yadda kwararru suka yi misali,” in ji shi.

Ya ce, KASU sabuwar jami’a ce kuma jami’a ta biyu da ake nema a jihar,  da Kuma jami’ar mafi saurin bunkasa a fadin Nijeriya, wadda aka kafa shekaru 18 da suka gabata.

tare da manyan malamai kamar su Farfesa Idris A. Abdulkadir, OFR da Farfesa Abubakar. A. Rasheed, MFR, a Matsayin kwamitin gudanarwa, ya kara da cewa malaman sun tabbatar da cewa ba a taba yin kasa a gwiwa ba wajen nada kwararrun malamai.

Sanarwa ta kara da shawartan  malaman jami’ar dake cikin kunjiyar da suyi tunanin kan jami’ar su da mutane da su fice da ga kungiyar.

Zafafa Labarai