Countdown
Connect with us

Labarai

Karancin Ruwa A Garin Kukui Ya Tilastawa Mazauna Garin Diban Ruwa Inda Dabobin Suke Sha

Published

on

Mazauna unguwar Kukui dake karamar hukumar Kagarko sun yi kira ga gwamnatin jihar da ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su kawo musu dauki.

Kukui village photo credit: kaduna political Affairs

Mista James Akaito, wanda ya taba zama Hakimin kauyen Kukui, ya bayyana cewa, saboda rashin kayan aiki na zamani, mazauna unguwar suke diban ruwan sha daga waje daya da dabbobin su.

Ya kara da cewa suna daukar sa’o’i da yawa kafin su bi ta ramukan domin isa ga rafi, tare da jefa rayuwarsu cikin hadari.

Wani mazaunin unguwar da yake zantawa da wakilin jaridar kaduna political Affairs ya ce, “Muna da rijiyoyin burtsatse da ba su da kyau.

Wasu daga cikin wannan rijiyoyin burtsatse ba su iya yin aiki har tsawon mako guda, suke tsayawa. Al’umma garin na kashe makudan kudade wajen gyara su amma wakan ba ya biyyan kudin sabulu.

Mun shigar da shugabanin kananan hukumomi ama abun yaki cin tura , shi ya sa muke son gwamnatin jiha ta taimaka wajen shawo kan matsalar ta hanyar Samar Mana rijiyoyin burtsatse Masu anfani da hasken rana, wadanda za su iya tanadin ruwa ga jama’armu.

Muna da guda ɗaya da ke aiki a halin yanzu kuma yana ɗaukar kusan awa ɗaya kafin ruwa ya faɗo don amfani da mazauna sama da 3000. Yawancin jama’a suna shan ruwa daga rafukan ne da dabobi ke sha.”

Photo credit: Kaduna political Affairs

Wani mazaunin garin, Mista Nuhu Dogo, wanda ya kasance shugaban matasa na al’umma, ya yi kira ga hukumar da ta kawo musu dauki, ya kara da cewa “Unguwarmu tana da karfin kada kuri’a, bai dace a yi watsi da mu ba.

An gano mana cututtuka daban-daban sakamakon gurbataccen ruwan da muke sha. Rijiyoyin burtsatse ba sa aiki.

Iyayenmu mata suna yin kasada da rayukansu don tafiya cikin dazuzzuka na sa’o’i don kawai su sami ruwa mara tsabta daga rafi. Ruwan da makiyaya ke ba shanunsu.

Muna kira ga gwamnati da ta samar mana da hanyoyin ruwa na zamani, amintattu. Abin da muke nema ke nan kuma ba na jin ya yi yawa in tambaya.

Zafafa Labarai