Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Mayan labarai guda biyar na ranar lahadi

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar lahadi.

  1. Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya kalubalanci dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, da yaje yayi hira a gidan talabijin na tsawon sa’a guda.
  2. Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya baiwa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu da ta gyara babbar hanyar Legas-Ota-Abeokuta da ta lalace. Ya sha alwashin daukar nauyin sake gina shi idan har Gwamnatin Tarayya ta gaza gyara shi a cikin wannan lokacin.
  3. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce Atiku Abubakar ya yi masa tayin takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2007. Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga hirar, inda Atiku, wanda yanzu dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP. , ya ce ya ki amincewa da Tinubu a matsayin abokin takarar sa saboda tikitin musulmi da musulmi.
  4. Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar NNPP ya hakarci bikin kadamar da sabon ofishin jam’iyar a Kaduna.
  5. Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana duk abin da ya faru a jam’iyyar PDP. Wike ya bayyana hakan ne a wani sakon Twitter da ya wallafa a yammacin ranar Asabar.

Zafafa Labarai