Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Mayan labarai biyar na ranar Juma’a

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Juma’a.

  1. Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) a jiya, ta amince da 140 zuwa sama a matsayin mafi karancin maki na kasa don shiga jami’o’in gwamnati a shekarar 2022. Hukumar ta amince da 100 ga kwalejojin ilimi, 120 na Polytechnics da 140 a jami’o’i.
  2. A ranar Juma’a ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta gurfanar da tsohon Akanta Janar na Tarayya Ahmed Idris , a gaban Mai Shari’a A.O. Adeyemi Ajayi na babbar kotun birnin tarayya Abuja, kan badakalar naira biliyan 109.
  3. An gano matashiya mai shekaru 15 da ake zargin wasu mutane hudu ne suka yi garkuwa da ita, amfani da kwayoyi da kuma yi mata fyade a yankin Igando da ke jihar Legas. An same ta bayan kwana biyar da bacewar ta.
  4. Gwamnatin tarayya ta yi hasashen kashe Naira Tiriliyan 6.72 kan tallafin da ake kira Premium Motor Spirit (PMS) a kasafin kudin shekarar 2023. Kudaden da aka yi hasashen kashewa ya haura N2.53trn fiye da adadin tallafin man fetur da ake sa ran zai kai har watan Mayun shekara mai zuwa.
  5. Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, ta ce babu dokar zama a gida a yau Juma’a. IPOB ta ce a yi watsi da umarnin da aka ruwaito wanda ake zargin almajirin Nnamdi Kanu, Simon Ekpa.

Zafafa Labarai