Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Mayan labarai biyar na ranar Asabar

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Asabar.

  1. Kungiyar manyan ma’aikata ta Najeriya Polytechnic (SSANIP) ta umurci mambobinta da su marar wa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC baya a wata zanga-zangar da ta shirya yi a fadin kasar saboda yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ba a warware ba. Ana sa ran gudanar da zanga-zangar a mako mai zuwa.
  2. Ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Najeriya (AON) sun sanar da jama’a da ke shawagi kan matsalar karancin man da ke damun jiragen, inda suka ce hakan zai haifar da katsewar jiragen a fadin kasar. A cikin wata sanarwa da kakakin AON, Farfesa Obiora Okonkwo, ya fitar, ya bayyana cewa fannin sufurin jiragen sama ya na fuskanta babban matsala sakamakon karancin man fetur din da aka fi sani da Jet-A1.
  3. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta mana suna da kuma tantance sahihancin Sadik Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano. Hakan ya haifar da rudani a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar masu biyayya ga zartaswar jihar karkashin jagorancin Shehu Sagagi.
  4. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce tikitin takarar musulmi da musulmi ya sanya shi kin amincewa da Asiwaju Bola Tinubu a lokacin da yake son zama mataimakinsa a shekarar 2007. Atiku, wanda ya taba zama mataimakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007. Ya bayana hakan a wata hira da yayi da Arise TV jiya.
  5. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar da su zabi jam’iyyar APC a zabe mai zuwa domin tabbatar da dorewar harkokin siyasa, da kwanciyar hankali a kasar da ma yankin yammacin Afirka. Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake karbar tawagar jihar Nasarawa karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule a fadar gwamnati da ke Abuja.

Zafafa Labarai