Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar talata

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar talata.

  1. Akalla manoma tara ne aka kashe a gonakinsu daban-daban a karamar hukumar Guma ta jihar Benue. Gwamna Samuel Ortom, wanda ya bayyana hakan a jiya, yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Makurdi, ya zargi makiyaya da hannu wajen kashe-kashen.
  2. Fasinjoji uku na jirgin kasa mai zuwa Kaduna da aka kai wa hari a watan Maris sun samu ‘yanci. An sako su ne sa’o’i 24 bayan ‘yan ta’addar sun fitar da wani faifan bidiyo mai tayar da hankali inda aka ga wadanda aka sace ana musu duka.
  3. Hon. Sani Liti, shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Katsina, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta yin murabus saboda ” gazawarsa wajen tabbatar da tsaron Najeriya “. Liti ya yi wannan kiran ne yayin ganawa da manema labarai a Katsina ranar Litinin.
  4. Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke Ado Ekiti ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan wani basaraken gargajiya. Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru bakwai ga kowane daya daga cikin mutane hudun da aka same su da laifin hada baki da kuma daurin rai da rai saboda yunkurin kashe wata mata.
  5. An harbe wani jami’in rundunar ‘yan sandan jihar Ondo a Najeriya. Jami’in da aka bayyana sunansa da Insfekta Temenu Boluwaji, an kashe shi ne a wani hari da aka kai wa Dibishin Okuta Elerinla da ke Akure, babban birnin Jihar a safiyar ranar Litinin.

Zafafa Labarai