Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: manyan labarai guda biyar na ranar talata

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Talata.

  1. Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar PDP a hukumance. Wannan dai na zuwa ne bayan watanni uku da komawar Shekarau daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
  2. Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar, tana neman a tasa keyar mataimakin kwamishinan ‘yan sandan kasar, Abba Kyari da aka dakatar zuwa kasar Amurka domin gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da laifin zamba ta yanar gizo. Alkalin kotun, Justice Inyang Ekwo ya yanke hukuncin ne a ranar Litinin.
  3. Kungiyar Malaman Jami’o’i ta sanar da yajin aikin gama-gari. An dauki matakin ne a wani taron majalisar zartarwa na kungiyar da aka gudanar ranar Lahadi a Abuja.
  4. Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a jiya, ta mayar da kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sheriff Oborevwori, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.
  5. Kalamai Bashir Elrufai, kan kunjiyar malaman jami’oi ASUU ta haifar da CeCe kuce a sahar dandalin sada zumunta.

Zafafa Labarai