Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar talata

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar talata.

  1. Jami’ar Kaduna (KASU), ta fara gudanar da jarabawa ga daliban ta a jiya 1 ga watan Agusta, 2022.
  2. Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kara tsawaita yajin aikin da ta keyi da wasu makwanni hudu . Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana matakin da kungiyar ta dauka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.
  3. Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammad Bello, a jiya, ya sake bude filin shakatawa na Millennium bayan shekaru biyu da rufe ta saboda COVID-19.
  4. Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ta ce a ranar Laraba za ta gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, mataimakin shugaban kasa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da kuma Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas. dangane da rikicin da ke kunno kai a jam’iyyar. Shugaban BoT, Sanata Walid Jibrin ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya.
  5. A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Joro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, inda suka kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu shida. Akalla mutane bakwai ne kuma wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka kashe a karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Filato.

Zafafa Labarai