Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar laraba

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar laraba.

  1. Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar da rahoton tsaro 44 kafin harin gidan yarin Kuje a Abuja. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayar da gudunmuwar kudirin dakatar da shirin hana amfani da babura a fadin kasar nan da gwamnatin tarayya ta yi.
  2. An sake sace Mrs Habiba Adamu, matar Ardon Fulani na karamar hukumar Kwali a Abuja, Alhaji Adamu Garba Ardo. Matar wadda aka yi garkuwa da ita a watan Fabrairu amma wasu ‘yan banga suka ceto ta, tare da ‘ya’yanta uku a daren Litinin.
  3. Kimanin mutane 36 mazauna unguwar Keke B a garin Millennium city, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, an ce an yi garkuwa da su. Lamarin dai, an tattaro cewa ya faru ne yayin da mazauna yankin da dama ke shirin yin barci a ranar Litinin.
  4. Sabbin kididdigar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta fitar, game da ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a, ta nuna cewa jihar Legas ta zarce jihar Kano, bisa ga adadin wadanda aka kammala rajistar. A yanzu Legas na da 508,936, sai Kano mai 500,207, sai Delta mai 481,929.
  5. Hukumar civil defense, NSCDC, ta baiwa dukkan jami’anta na Jihohi umarni su kasance cikin shirin ko ta kwana, biyo bayan samun rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu ‘yan ta’addan Boko Haram, da na yankin ISWAP, sun kara kaimi wajen kai hari a babban birnin kasar. , Abuja, da wasu Jihohi biyar, ciki har da Legas.

Zafafa Labarai