Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar Lahadi

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Lahadi.

  1. A ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar matasa masu yi wa kasa hidima ta kasa ta yi alhinin ganin gawar mai suna Eunice Igweike, da ake zargin an kashe ta a yayin da take hanayar tafiya sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC da ke Sagamu jihar Ogun. Igweike, memba na Batch B 2022, wace ta kammala karatunta a Federal Polytechnic Oko, jihar Anambra.
  2. Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki kauyen Shika da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da matar wani ma’aikacin Nuhu Bamalli Polytechnic da wasu yara uku. Wani mazaunin yankin, Alhaji Bawa Idrisu, ya ce masu garkuwan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 11 na ranar Juma’a, inda suka nufi gidan mutumin kai tsaye suka yi awan gaba da mutanen hudu.
  3. A jiya ne aka kama wasu mata biyu, wanda rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama bisa zargin sace wani jariri a jihar Ogun. An tattaro cewa an ga daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Chinyere Nwozu mai shekaru 53 tare da jaririyar mai mako daya tana kuka da misalin karfe tara na safe.
  4. A ranar Asabar ne Najeriya ta samu lambar yabo ta farko a gasar Commonwealth da ke gudana a birnin Birmingham na kasar Birtaniya. Adijat Adenike Olarinoye ta amu nauyin kilogiram 203 a gasar daga nauyi kilo 55 na mata inda ta lashe lambar zinare ta farko a Najeriya a wasannin.
  5. Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan, a ranar Asabar, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa yana zaune kan wasikun sauya sheka daga Sanatocin da bai so ya bayyana a zaman majalisar ba. A wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman (Media), Mista Ola Awoniyi ya fitar a ranar Asabar, Lawan ya ce, dokokin majalisar ba su ba shi damar musanta karanta wasika daga kowane Sanata ba.

Zafafa Labarai