Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar Asabar

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Asabar.

  1. Kasa da sa’o’i 48 kafin a kammala aikin rajistar masu kada kuri’a, ‘yan Najeriya a jiya, sun yi tattaki zuwa cibiyoyin rajistar masu kada kuri’a a fadin kasar, domin suyi rijista kati masu kada kuri’a, wato PVC. Yawancin, duk da haka, sun bar cibiyoyin saboda rashin iya yin rajista.
  2. Gamayyar Kungiyoyin Arewa 52 (CNG), a ranar Juma’a, ta yi watsi da kiran da Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta yi na a saki jagoran ‘yan awaren Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, ba tare da wani sharadi ba. Sun kuma zargi Majalisar Dinkin Duniya da nuna son kai a wasu yankuna na kasar.
  3. Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a ranar Juma’a sun kai farmaki Wuse shiyya ta 4 a babban birnin tarayya Abuja, cibiyar yawancin masu gudanar da canji a Abuja sakamakon faduwar darajar Naira da ake ci gaba da yi.
  4. Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), a jiya, ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa kada su zabi duk wani tikitin da bai cakude tsakanin Kirista da Musulmi ba a zaben 2023. Lawal ya ce, za a bijire wa tikitin tsayawa takara Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC da addu’a da kuma katin zabe (PVC).
  5. Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya amince da sake sauye sauye aiki jami’ai a rundunar sojojin Najeriya a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin tsaro a ƙasar. Da yake magana a karshen taron tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce kasar na cikin wani mawuyacin hali.

Zafafa Labarai