Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan Labarai guda biyar na ranar alhamis

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar alhamis.

  1. Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takararta mataimaki shugaban kasa a zaben 2023. An bayyana Shettima ne a wani taron da aka yi a Abuja ranar Laraba.
  2. A jiya ne zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC). An ba shi takardar shaidar ne a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
  3. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin ci gaba da jajircewa da biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Tinubu yayi magana ne a fadar shugaban kasa a ranar Laraba lokacin da ya raka abokin takararsa, Kashim Shettima don ganin shugaban kasa.
  4. Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a ranar Laraba sun yi taho-mu-gama kan kin amincewa da yadda kungiyoyin suka ki yin watsi da zanga-zangar da ta shirya yi na tsawon kwanaki biyu a fadin kasar da aka shirya gudanarwa a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli. Kungiyoyin kwadagon da suka hada da ma’aikatan jirgin sama kasa da wasu 40 ne za su halarci gangamin da aka shirya. tare da hadin kai da malaman jami’o’i masu yajin aiki.
  5. DCP Abba Kyari da aka dakatar ya bayar da labarin yadda ya buya daga ‘yan ta’addan da suka Kai hari gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja. A ranar 5 ga watan Yuli, kungiyar Boko Haram da ta balle (ISWAP), ta jagoranci kai hari a cibiyar.

Zafafa Labarai