Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar Alhamis

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Alhamis.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci hafsoshin tsaron sa domin yin taron gaggawa a yau Alhamis. Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 48 bayan harin da ‘yan ta’addan suka kai wa dakarun tsaron fadar shugaban kasa a Abuja babban birnin kasar.
  2. A jiya ne ‘yan majalisar dattawan jam’iyyar PDP suka ficce daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu da karuwar rashin tsaro a Najeriya. Sanatocin sun bayyana cewa sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida domin ya magance hare-haren ta’addanci a kasar ko kuma a tsige shi.
  3. Biyo bayan kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasar nan, gwamnatin jihar Nasarawa ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a fadin kananan hukumomi 13 na jihar, a matsayin wani mataki na kare rayukan dalibanta.
  4. Gwamna Nasir El-Rufai ya yi barazanar korar daukacin malaman jami’ar jihar Kaduna (KASU) da ke kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU). Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu saboda gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu.
  5. Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai ya bayyana cewa ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyun adawa da a ranar Larabar da ta gabata suka baiwa shugaban kasar wa’adin makonni shida ya magance matsalar rashin tsaro a kasar nan ko kuma a tsige shi suna wasa ne. Ya ce su ‘yan tsiraru ne kuma ba za su iya samun hakan ba.

Zafafa Labarai