Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manyan labarai guda biyar na ranar Alhamis

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar Alhamis.

  1. Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta ci tarar Naira miliyan 5 a gidan Talabijin na Trust Television Network (Trust TV) a kan yada wani shirin mai suna “Nigeria’s Banditry: The Inside Story”, wanda gidan rediyon ya nuna a ranar 5 ga Maris, 2022.
  2. Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana neman fitaccen shahararren dan Najeriya, Ismaila Mustapha, wanda aka fi sani da Mompha, a shafinta na Instagram. Ta bukaci ‘yan Najeriya da ke da bayanin inda Mompha yake da su yi magana ko tuntubi ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
  3. Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban makarantar kididdiga ta Manchok da ke karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna. Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wani mazaunin garin yayin harin da aka kai ranar Litinin.
  4. Wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun yi garkuwa da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Anambra, Benson Nwawulu. Majiyoyi sun ce an yi garkuwa da Nwawulu, dan majalisa mai wa’adi biyu a majalisar dokokin jihar a gidansa da ke Ihiala ranar Lahadi.
  5. A jiya ne ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta tabbatar da bayar da gudummawar Naira biliyan 1.14 ga jamhuriyar Nijar domin taimakawa wajen sayen wasu motoci aiki.

Zafafa Labarai