Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

Kanun Jaridu: Manyan Labarai biyar na ranar Juma’a

Published

on

Barka da safiya ! Wadanan sune manyan labarai guda biyar daga kanu Jaridu.

  1. Cibiyar Haɓaka sha’anin Demokradiya, Centre for Democracy Development (CDD), ta bayana cewa akwai yuwar asamu magudi, tare da siyan Kuri’u a zaben ranar sati na jihar Osun. Prof. Victor Isumonah, memba cibiyar ne, ya bayana haka a ranar Alhamis a Abuja.
  2. Hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta bayana cewa ba aikin ta bane hana siyan Kuri’u a yayin zabe. Prof. Abdulganiy Raji na jihar Osun ya fadi haka yayin hira da gidan telebijin Channel a cikin shirin Sunrise Daily na safiyar Alhamis.
  3. Shugaba Buhari ya umurci jami’an soji da su kawo karshen ‘yan ta’ada a fadin kasa baki daya. Buhari ya bada Umarni ne a yayin bikin yaye manye jami’ai 247 da ya gudana a bariki Jaji dake Kaduna.
  4. Antoni Genar kuma Kwamishina Sharia na jihar Borno, Barista Shehu Lawal shi aka zaba don miye gurbin kujera Sanata Borno ta tsakiya a jam’iyar APC a zaben 2023. Lawal zai maye gurbin Sanata Kashim Shatima, wanda aka zaba matsayin mataimaki shugaban kasa.
  5. Aqala mutane biyu sun jikata a yayin harin ‘yan bindiga kan jami’an hukumar zabe INEC a karamar hukumar Igboeze North ta jihar Inugu. Festus Okoye, ya sanar da hakan a wata sanarwa da yafitar a ranar alhamis.

Zafafa Labarai