Countdown
Connect with us

Kanun Jaridu

KANUN JARIDU: Manya labarai guda biyar na ranar litini

Published

on

Jama’a barka ku da safiya, Muna dauke muku da manyan labarai guda biyar na ranar litini.

  1. Shahararren dan fashin nan, Ado Aleiro, wanda aka nada a matsayin Sarkin Fulani a kwanan nan a masarautar Yantodo ta jihar Zamfara, ya ce bai nemi mukamin ba. Dan fashin wanda ake zargi da ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yamma, ya bayyana haka ne a wata hira da DW Hausa.
  2. Makonni kadan bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, ‘yan ta’adda sun yi barazanar sace dan Najeriya na daya. A wani sabon faifan bidiyo, ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 na jirgin kasa na Abuja Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar yin garkuwa da Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai tare da kashe su.
  3. A yau ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, za ta gana da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da sauran su, domin kawo karshen taron zanga zangar hadin kan da majalisar ke shiryawa domin nuna goyon baya ga kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in ke ci gaba da yi. An tattaro cewa, za ayi taron ne domin a amince da tsarin da zanga-zanga zai gudana da kuma inda masu ruwa da tsaki za su hadu domin gudanar da ranakun da aka ambata.
  4. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Nasiru Ila a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai ta kasa. Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
  5. Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ba a samu asarar rai ba a lamarin da ya faru da wani mutum da budurwarsa a wani shingen bincike na ‘yan sanda a babban birnin jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar ranar Lahadi, a Enugu.

Zafafa Labarai