Countdown
Connect with us

Illimi

Kaduna Politeknik tafara bada gurbin karatu shekara 2021/2022

Published

on

Kofa daga ga cikin kofofin shiga Kaduna Politeknik

Hukumar makaranta Kimiya da fasaha na Gwamnatin Taraya, Kaduna Politeknik, Kaduna, tafara bada guraben karatu shekara 2021/2022 ga dalibai.

Rohotoni sun bayana cewa, makaranta tafara bada guraben karatu ne a ranar litini 23 ga watan Mayu, 2022.

Saidai guraben karatun da aka fara saki na dalibai ne masu son karatun a bangaren babar difloma (HND).

A wani bincike da jaridar kadunareporters tayi ta gano cewa, ka wo yanzu yan tsangayar Computer Science da Architecture ne aka fara bawa guraben karatu.

Don haka dalibai da suka san sun nema guraben karatu a makarantar da su kwantar da hankalin su, sanan su cigaba da duba shafin gurbin karatu malakin makarantar akai akai.

Hanyoyin da dalibai zasu bi gun duba matsayin gurbin karatun su a makarantar Kaduna Politeknik;

Dalibai su ziyarci shafin makarata a kan adireshi yanargizo www.kadunapoly.edu.ng .

Dalibai su nema gurin da akayi wa lakabi da “ADMISSION” su dana shi.

Dalibai zasu ga inda akasa ” CHECK MY ADMISSION STATUS” sai su taba gun.

Dalibai zasu sanya numbar application dinsu ga yan bangaren babar difloma, sai kuma number JAMB ga dalibai Yan difloma.

Sai dalibai su danan alamar bincika don ganin matsayin gurbin karatun su.

Zafafa Labarai