Countdown
Connect with us

Siyasa

Jam’iyar LP ta dage shirin tataki mutum miliyan biyu domin Peter Obi a Kaduna

Published

on

Jam’iyar Labour Party (LP), ta dage ranar gudanar da shirin tataki na mutum miliyan biyu domin dan takara shugaban kasa Peter Obi a Kaduna.

Bayanin dage shirin tataki na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hanu shugaban matasa jam’iyar na Kaduna a ranar Juma’a.

Kwamurade Austin Aniagu, a cewar sa dage taron ya biyo bayan shawarwari ne da suka samu daga jami’an tsaron jihar Kaduna wanda hakan ya basu dama su kara komawa domin sake fasali tare da fito da sabin shirye shirye kan batun tatakin.

A cewar sanarwa, ” muna sanar dacewa a dage ranar tataki mutum miliyan biyu da yakamata ya guda na a ranar 27 ga watan Agusta 2022 a kaduna zuwa wani lokaci, za Kuma a sanar da sabon ranar na gaba kadan.

Hakan ya biyo bayan shawarwari da muka samu daga jami’an tsaron, kuma zai ba mu damar sake sabon tsari da shirye shirye.

Muna kira ga matasan jam’iyar da su kasan ce cikin shiri domin gudanar da tataki .”

Jihar Kaduna ta kasance jihar mataimaki Shugaban kasa na jam’iyar a zabe 2023.

Zafafa Labarai