Countdown
Connect with us

Illimi

Jami’ar Kaduna ta kafa kwamiti tabatar da zaman lafiya da hadin kai

Published

on

Shabon shugaban Jami’ar Kaduna (KASU), Prof. Ashafa ya kadamar da sabon kwamiti domin tabatar da hadinkai da zaman lafiya tsakanin Jami’ar da unguwannin ma kwabta ta.

Mai magana da yawun bakin Jami’ar, Adamu Nuhu Bargo ne ya tabatar da hakan a wata sanarwa da yafitar a Kaduna.

Bargo ya ce, ma qasudin kafa kwamiti shine don ganin a samu zaman lafiya tsakanin makwabta Jami’ar tare da tattauna duk wata matsala da Kan ta so a tsakani.

Ya Kara da ce wa aikin kwamiti zai hada da bada shawara ga shugaban Jami’ar tare da shawo Kan matsaloli da Kan taso domin tabatar da cigaba da zaman lafiya.

Prof. Ahmed Babajo shine shugaban kwamiti tare da Prof. Ibrahim Sodangi a matsayin mataimaki shugaban sai Sadiya Jimen a matsayin sakatariya.

Sai Kuma mambobi da suka hada da wakilan kungiyar malamai rashen Jami’ar ASUU, SSANU, NASU, NAAT, SUG da kuma wakilan dalibai ban garen adina’i.

Zafafa Labarai