Countdown
Connect with us

Illimi

Jami’ar Kaduna ta fara gudanar da jarabawa ga dalibai ka’in da Na’in

Published

on

Jami’ar Kaduna (KASU), Kamar sauran jami’oi a Nijeriya, ta shiga yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Faburairu 2022.

A jiya 1 ga watan Agusta, 2022 jami’ar ta fara gudanar da jarabawa Kamar yadda ta sanar a sabon jadawalin cigaba da karatu.

Wakilin mu ya tabatar mana da cewa daliban department din Hausa, Biology, English And Drama, sai wasu daga jami’ar dake kafanchan ne suka fara rubata jarabawa a jiya.

Kamar yadda sabon shugaban jami’ar, Prof. Ashafa ya tabatar da cewa ASUU-KASU bata da iko hana hukumar jami’ar gudanar da jarabawa.

Daga baya bayan nan, Gwamna jihar ya sha alwashin korar Malamai dake karkashin kungiyar ASUU-KASU matsawar suka cigaba da yajin aiki.

Inda ya Kara dacewa kuma zai cire albashi malaman da suka karbi albashi suna yajin aiki, domin dokar kasa tace kada abiya albashi ga ma’aikaci dake gudanar da yajin aiki. Inji shi.

A jiya ne dai kungiyar malaman jami’oi ASUU takara wa’adin yajin aikin da takeyi da makoni hudu.

Zafafa Labarai