Countdown
Connect with us

Tsaro

Jami’an tsaro sun kashe, tare da dakile harin ‘yan bindiga akan titin Abuja zuwa Kaduna

Published

on

Jami’an ‘yan sanda Hoto: KOLA SULAIMON/AFP Asali: Getty Images

Rundunar yansanda Jihar Kaduna, tace Jami’an tsoran hadin gwiwa sun dakile harin garkuwa da mutane a kan titin Abuja zuwa Kaduna a ranar lahadi. Kamar yada jaridar Daily Post ta ruwaito.

A cewar DSP Mohammed Jalige, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ‘yan sandan sun kuma kashe daya daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Ya ce tawagar jami’an tsaro sunyi arangama da ‘yan bindiga da ke kan aikin ta’adanci a wani yanki inda nan take suka yi musayar wuta da su, lamarin da ya kai ga kashe daya daga cikin ‘yan bindigar.

Ya ce sauran ‘yan bindigar sun ja da baya suka tsere zuwa cikin dajin, inda ya kara da cewa bayan bincike da aka yi a yankin, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK47 da kuma babura na ‘yan fashi guda tara (9).

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yekini Ayoku, ya yi matukar farin ciki da jajircewa da rundunar hadin gwiwa ta nuna, ya kuma ba su tabbacin cewa sadaukarwar da suke yi na tabbatar da tsaron lafiyar jama’a ba zai tafi a banza ba.

Ya ce wadanda suka jikkata cikin ‘yan bindigat za su rika zagayawa a cikin al’ummomin da ke kusa da su don samun duba lafiyar su, kamar yadda ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani mutum ko kungiyar da ke jinya raunukan harbin bindiga ga jami’an tsaro mafi kusa.

Zafafa Labarai