Countdown
Connect with us

Illimi

JAMB ta bayana dalibai da sukafi ci maki a Jarabawar 2022

Published

on

Rijistara JAMB yabayana cewa dalibai 378,639 cikin1,761,338 da suka sama damar rubuta jarabawa JAMB na shekara 2022 ne sukayi nasara samu maki 200 zuwa sama.

Rijistara ya bayana hakan ne a gun taro masu ruwa da tsaki don kayada adadin maki na shekara 2022.

A dadin dalibai 520,596 ne suka samu maki 190 zuwa sama, dalibai 704,991 ne suka samu maki 180 zuwa sama, dalibai 934,103 ne suka samu maki 170 zuwa sama sai kuma daliban da adadin su yakai 1,192, 057 suka samu maki 160 zuwa sama.

Ya Kara da cewa wani dalibi Mai suna Adebayo Eyimofe, dan asalin jihar Ekiti ne yafi ko nasara a jarabawa ta 2022 inda yasamu maki 362.

Sai kuma Ugwu Chikelu, dan asalin jihar Enugu ke bin sa abaya da maki 359.

Sauran dalibai dake biye da su sun hada da Igbalaye Ebunoluwa 357; Emmanuel Oluwanifemi 357; Ozumba Samuel 357; Olumide-Attah Ayomide 355; Lawal Olaoluwa 355; Dokun Jubril 354; Amaku Anthony 354 da kuma Aghulor Divine 353.

Zafafa Labarai