Countdown
Connect with us

Illimi

JAMB ta amince da maki 140 a matsayin maki mafi karanci na bada gurbin karatu 2022

Published

on

Hukumar gudanar da jarabawa JAMB da masu ruwa da tsaki sun amince da maki 140 a matsayin maki mafi karanci gun bada guraben karatu na shekarar 2022.

Hukumar sun cima matsayar ne yau alhamis, a garin Abuja a gurin taron masu ruwa da tsaki kan batu bada guraben karatu.

Hukumar ta tsayar da adadin maki mafi karanci ga masu neman guraben karatu a jami’oi da kuma kwalejin Illimi, da makaratun fasaha da kimiya na shekarar 2022.

An tsada wa jami’oi maki 140 mafi karanci sai maki 120 ga makarantu kimiya da fasaha (Foliteknic’s), sai maki 100 ga makarantu kwalejin Illimi.

Taron wanda Minista Illimi, Adamu Adamu ya jagoranta.

A yayin jawabin sa Minista Illimi, Adamu Adamu, ya ja kune ga hukumar makarantun gun bada guraben karatu ta barauniyar hanya.

Yace dole ne dukan guraben karatu kama daga jami’oi, kwalejin Illimi da makaratun kimiya da fasaha su zama anba da su ta shafin bada guraben karatu na bai daya wato CAPS.

Zafafa Labarai