Countdown
Connect with us

Labarai

Iyayen dalibai sun gudanar da zanga zanga kan hana yaran su zana jarabawar WAEC saboda rashin Kamala rijista, sakamokon harin ‘yan bindiga a Kaduna

Published

on

Zanga zangar iyayen dalibai Hoto: SaharaReporters Asali: SaharaReporters

Wasu daga cikin iyayen dalibai da ba su sama damar zana jarabawar WAEC a bana ba sun gudanar da zanga zanga, a ofishin hukumar jarabawar WAEC dake garin kaduna a ranar asabar.

Jaridar SaharaReporters ta rawaito cewa, iyayen sun gudanar da zanga zanga ne a Kofar shiga harabar ofishin hukumar dake Kaduna dan nuna damuwar su.

A cewar wani, daliban da abun ya shafa sun biya kudin fom din zana jarabawar, sai dai sun samu matsaloli ne gun rijista wanda yayi sanadiyar hanusa kamala rijista.

Wasu kuma sun bar yakin da suke sakamokon hare haren ‘yan bindiga, haka zalika hukumar jarabawar ta rufe shafin rijista jarabawa da wuri.

Makaratu da abun ya shafa sun hada da; Kalhyatu Abdurahman Bin Auf Academy, Jere; Al-bameen Academy, Kaduna Nigeria; Government Senior Secondary School, Iddah; Government Secondary School, Kagarko; Government Secondary School, Kuse; ECWA Secondary School, Kubacha; Government Secondary School, Independence Way; Great Panaf Schools, Kaduna South, and Government Secondary School, Maro.

Sai dai hukumar makarantu sunce sun rubuta wasika ga shugaban Hukumar Jarabawar Ta Kasa, ta karkashin Ofishin Ministan Illimi, sai dai basuji wani sako ba gameda wasikar da suka aika.

Sun rubuta wasika ne tun 12 ga watan Afrilu, dauke da sunayen makarantu da na daliban da abun ya shafa, sai dai har wa yau basuji wani kira ko sako ba daga hukumar.

Abinda yasa iyayen gudanar da zanga zanga shine, yadda zonal codinato, yace za aba daliban dama rubuta Jarabawar Nov/Dec ama sai sun sake biya kudi, wanda hakan ba adalci bane. Cewar wani daga cikin su.

Kimani dalibai dari 700 ne abun ya shafa a dukan makarantu , inda makarantu sun biya ma dukan su kudin fom din jarabawa ga hukumar.

Zafafa Labarai