Countdown
Connect with us

Labarai

Iyalan Marigayi Abacha, Sun maka Gwamnati Jihar Kaduna a Katu Kan kwacen fili

Published

on

Hajiya Maryam Abacha Hoto: Jardar Thisdaylive

Iyalan Marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soji, sun maka Gwamnati Jihar Kaduna a gaban kotu, Kan batun kwace musu wani fili dake unguwar rimi a cikin garin Kaduna.

Maryam Abacha, uwargidan Marigayi Janar Abacha, tare da baban dan ta Alhaji Muhammad Sani Abacha, da sauran iyalai ne suka shigar da kara a gaban kotu.

Sun shigar da karar ne don neman kotu ta tirsasa wa Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagoranci Gwamna Nasiru Ahmed Elrufai, dawo musu da fili su da aka kwace.

Fili dai a cewar su, an karbe shi ne tun lokacin da Gwamna Elrufai, ke zango mulkin sa na farko.

Zafafa Labarai