Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Hon. Ashiru Kudan, Ya za gaye Kananan Hukumomi dake Jihar Kaduna a kwana Biyar Domin Ganawa Da Delegates

Published

on

Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan hoto: Engr Auwal-bz Nuhu Asali: Facebook

Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan, dan takara kujerar gwamna Jihar kaduna, a karkashin jam’iyar PDP, ya zagaya kana nan hukumomi 23 dake fadin jihar kaduna domin neman goyon bayan delegates.

Kudan, yafara ziyarar kananan hukumomi ne a ranar litini 9 ga watan Mayu, 2022 inda yafara da karamar hukumar igabi, Zaria, Sabon Gari, yayin da ya kamala zagayen a ranar juma’ah 23 ga watan Mayu, 2022 a karamar hukumar kaduna ta kudu, ta arewa da Kuma chikun.

Anasa ran Rt. Hon. Kudan, zai kai ziyarar karamar hukumar Birnin Gwari, a gobe sati domin neman goyon bayan mutanan yakin.

Ashiru Kudan, shine dantakarar da ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyar PDP a zaben shekarar 2019, Yayin dayayi rashin nasara a zaben Gwamna, inda jam’iya APC ta lashe zaben, Elrufai yazama Gwamana a karo na biyu.

Zafafa Labarai