Countdown
Connect with us

Rahotoni

Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutum 600 tare da raunata 2310 a watanin 6 a kan hanyar Kaduna zuwa Kano – Hukumar FRSC

Published

on

Jami’an Hukumar kiyaye Hadura yayin gudanar da aikin su

Tsakanin watan Janairu zuwa yuli 2022 mutum 600 Suka muta yayin da mutane 2310 suka samu raunika a sanadiyar hadarin moto akan titin Kaduna – Zaria -Kano.

Jami’in kiyaye hadura (FRSC) dake kula da zone 1 ACM DR Godwin Omiko, ya bayana haka a lokacin da ya ziyarci Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamali, a fadar sa dake Zaria.

Omiko yace Karin mutum 2310 ne suka samu munanan raunuka sanadiyar hadaruruka a tsakanin watanin.

Yace a wata yuli 2021, mutum 350 suka rasa rayukan su, wanda yanzu ansamu kari sosai wanda yana bukatar wayar da kai.

Zonal Kwamandan mai kula da Jihar Kaduna, Katsina, Kano da Jigawa, ya bukaci sarakin da ya shigo ciki lamarin da shawo kan matsalar.

Omiko yace yawanci hadaruruka na faruwa sabida tukin ganganci, rashin bin ka’idar tuki, tuki cikin maye, gudu na wuce misali.

Yayin maida jawabi, Sarki Bamali ya ba ma hukumar tabaci cewa masarautar Zazzau zatayi anfani da hayoyin isar da sakonta zuwa ga masu aikin tuki don shawo kan matsalar.

Zafafa Labarai