Countdown
Connect with us

Labarai

Harin Jirgin Kasa: Macizai sun fara cizon wanda akayi garkuwa dasu – Mamu

Published

on

Tukur Mamu ya bayana cewa macizai sun fara cizon mutane dake tsare a hanu ‘yan bindiga da sukayi garkuwa da su a harin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna.

Mamu, ya kasance mawalafi kuma dan Jihar Kaduna, Kuma shine ya jagoranci sulhu da yayi sanadin kubutar mutum 11 daga cikin fasinjoji da aka sace.

Mamu ya bayana hakan ne ga manema labarai a ranar litini a Kaduna.

Yace, akwai macizai dayawa a cikin daji da ake tsare da fasinjoji, macizan kuma suna zuwa ne da dare.

” Ina Baku tabacin cewa akwai macizai dayawa a dajin da fasinjoji suke, macizan sun na zuwa da dare kuma sun sari wasu daga cikin fasinjoji. magunguna gargajiya ake ba ma wa inda macizan suka Sara.

” Munsani cizon maciji na iya Kai ga rasa rai. Gwamnati ne kadai take da iko da karfin kawo karshen wanan lamari. Inda aka bi matakan da su ka dace, Ina baku tabacin za a shawo karshen faruwar lamarin cikin kwana ki ko sati. Ga misali Nan kan kubutar da mutum 11.” Inji shi.

Rashin isheshen kayan jinya, abinci mai kyau tare da tsaftacecen muhali ya kara sa su a wani hali.

Ya tabatar ma da yan uwan wanda ake rike dasu cewa babu daya daga cikin su da ake duka ko cin zarfin sa, saidai wurin da ake tsare da su ne bashi da kyau.

Zafafa Labarai