Countdown
Connect with us

Labarai

HAJJ 2022: Za afara jigilar rukuni farkon na maniyata 400 daga Kaduna zuwa Saudiya a ranar talata

Published

on

A yau talata ana sa ran fara jigilar rukunin farko na maniyata 400, daga karamar hukumar Igabi, Ikara, Giwa da wasu daga Zaria zuwa kasa Mai tsarki, domin gudanar da aikin hajin bana.

Sakataren hukumar Alhazai na Jihar Kaduna, Dr Yusuf Yakubu Arrigassiyyu, ya sanar da hakan yayin zanta wa da ma’aikata 81 na hukumar, Kan shirin bana.

Yace, ” in har komai yatafi daidai yada aka tsara, a yau talata kamfani jirgin Air Azman zai fara jigilar maniyata jihar Kaduna zuwa kasar Saudiya. Maniyata sun Gama shiri tsaf kawai jira suke afara jigilar su.

“Kamar yadda zaku ke gani, maniyata mu na sasansani alhazai dake Mando, inda ma’aikata mu ke musu gwajin karshe na Covid-19, wanda wajibi ne sai an ma kowane maniyaci kafin Isa kasar Saudiya.

Hukumar a shirye take dafara jigilar, ya kara dacewa, an samu tsaiko ne daga kamfani jirgin, saidai yanzu haka kamfani jirgin ya shedawa hukumar cewa ya shirya tsaf Kuma zai fara jigilar a ranar talata.

Arrigassiyyu, ya Kara bada tabacin cewa dukan maniyata Jihar Kaduna zasu tashi ne a filin jirgin sama na Jihar Kaduna ba na Aminu Kano ba.

Ya gargadi masu aikin duba lafiya da su tabatar sun tsaurara duba maniyata mata, domin tabatar da babu mace Mai juna biyu da akabari taje aikin hajji bana.

Ya ja kunan ma’aikata da su kiyaye tare da bin dokokin da aka shar’anta musu, domin za su hukunta duk Wanda ya saba doka Kamar yadda doka ta tanadar.

Zafafa Labarai