Countdown
Connect with us

Labarai

HAJJ 2022: wata mahajaciya Jihar Kaduna ta rasu a fillin arfa a garin Makkah

Published

on

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ta tabatar da rasuwar wata mahajaciya a ranar arfa a birnin Makkah.

Hukumar ta sanar da hakan me a ranar juma’a 8 ga watan Yuli.

Allah ya yi wa wata mahajaciya jihar Kaduna rasuwa a yau a filin Arafat dake birnin Makkah

Asiya Aminu daga karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna ta rasu a Arafat jim kadan bayan ta ga taimaka wajen rabon abinci ga alhazai a tanti.

Da yake tabbatar da rasuwarta, Ag Daraktan ayyuka na , Alh Abubakar Alhassan ya ce a safiyar ranar arfa ne, mahajaciya suka je Jabbal Rahma (dutsen rahama) inda ta koma tantinta.

Ta rasu ne a cikin tantin ta batare da fama da wata matsala rashin lafiya ba.

Zafafa Labarai