Countdown
Connect with us

Labarai

HAJJ 2022: Rukuni alhazai na biyu na jihar Kaduna sun sauka a tashar jirgin Aminu Kano

Published

on

Kimani alhazai 400 na jihar Kaduna rukuni na biyu sun dawo Nijeriya cikin koshin lafiya bayan kamala aikin Hajj a kasar Saudiya.

Alhazan dai sun sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano a safiyar asabar 23 ga watan yuli, da misalin karfe hudu

Kamfani jirgin Air Azman wanda shine yayi jigilar kwashe alhazai daga Kaduna zuwa kasa mai tsarki shike jigilar dawo da su a jirgi Mai lamba A340-600.

A ranar Alhamis ne dai rukunin farko na alhazai suka fara isowa Nijeriya ba yan kamala aikin Hajj bana.

Rukuni na biyu ya hado da alhazai karamar hukumar Giwa, Soba, Lere da kuma Kagarko.

Kimani alhazai 790 ne na Jihar Kaduna suka iso Nijeriya, yayin da za acigaba da kwaso sauran.

Zafafa Labarai