Countdown
Connect with us

Labarai

HAJJ 2022: Rukuni alhazai farko na jihar Kaduna sun dawo gida lafiya

Published

on

Kimani alhazai 390 na jihar Kaduna sun dawo Nijeriya cikin koshin lafiya bayan kamala aikin Hajj a kasar Saudiya.

Alhazan dai sun sauka a filin jirgin sama na jihar Kaduna a jiya alhamis da misalin karfe biyar da minti arba’in da biyar na yama.

Kamfani jirgin Air Azman wanda shine yayi jigilar kwashe alhazai daga Kaduna zuwa kasa mai tsarki shike jigilar dawo da su.

A ranar talata 21 ga watan yuni dai jihar Kaduna ta fara kwashe alhazai ta zuwa kasa mai tsarki don gudanar aikin hajjin bana.

Inda akafara da kwashe yan karamar hukumar Igabi, Ikara, Giwa da Zaria zuwa kasar Saudiya.

Zafafa Labarai