Countdown
Connect with us

Labarai

Hajj 2022: maniyata 2 sun rasu a kaduna

Published

on

Maniyata biyu Yan karamar hukumar Igabi Jihar Kaduna, Yakubu Abdulsamad da kuma Haruna Suleiman sun rigamu Gidan gaskiya.

Rahotonin sun bayana cewa daya ya muta a ranar lahadi daya kuma ranar litini, kafin tafiya kasar Saudiya don gudanar da aikin Hajj.

Ofisa me kula da rajista yan karamar hukumar Igabi, Aminu Surajo, shine ya tabatar da mutuwan su, kuma ya ce tuni anyi musu jana’iza kamar yadda addini musulinci ya tanadar.

Mutane biyu daga cikin maniyata rukuni farko da ake sa rai za a fara jigilar su suwa kasa Mai tsarki.

Kimani maniyata Jihar Kaduna 2,491 ake sa ran zasu Yi aikin hajji bana.

Mukadashin Gwamna Jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta yi kira ga maniyata rukuni farko da su samar da wakilci na gari a yayin gudanar da aikin hajji.

Balarabe, yayi da ta kai ziyarar bankwana a maniyata a Sansanin alhazai dake Mando, ta ce wa maniyata da su roka ma Jihar Kaduna zaman lafiya tare da kasa baki daya.

Zafafa Labarai